“Mace mai ilimi tare da aiki da ilimin tafi kowa tsada a duniya”- Hajiya Uwa Idris

TARIHINA

Tarihina shine an haife ni a Zaria watan july 1960.Na taso a Kaduna, kuma anan nayi firamare da sakandare. Naso in karanta law, sai daga baya na gane ba wannan hanyar nake son bi ba, sai na so chanjawa zuwa turanci amma bai yiwu ba, don lokacin nayi aure, sai ga juna biyu, daga nan ban sake yunkurin karatu ba.Amma duk da ban yi wani nisan karatun boko ba, ina alfahari da wanda na dan yi domin yana amfana ta.

ILIMINA

Ilimina zai ba mutane mamaki matuka, domin a duniya na neme shi, ba a makaranta ba. Na yi karatu sossai, amma ba a aji ba! Na karanta psychology, watau ilimin dabi’an dan adam kuma nayi shi ta littafai ba a makaranta ba. Na kuma yi makarantar duniya sossai in da Allah Ya Bani darrusa kala-kala na rayuwa.

Wannan shi ne ilimina.

BURINA INA KARAMA

Burina ina karama shine, a sanni ko ina, ma’ana inyi suna. Ban san dalili ba, amma haka na kan yi fata. Burina na son ayi ta maganata ta alheri, kuma in rinka tattauna matsalolin mutane ina bada shawara. Shi yasa ma na fara rubutu don neman cika wannan buri.

KALUBALE NA A RAYUWA

Akwai su kala-kala, amma babban kalubale na a rayuwata shine RASHIN A FAHIMCE ni a rayuwa. Idan nayi nan, sai a ce can nayi! An cika mani mummunan fahimta. A gida da waje haka nake, dalilin haka naga abubuwa da yawa, saboda komai nayi sai an mashi kwaskwarima. Mutane kuma ba sa mani da kyau ba wajen yin mani dauka daban da yadda nake. A ganina wannan jarabawa ne.

NASARORINA

Akwai kadan. Na farko yadda na zama tamkar wadda tayi dogon karatu har ana kira na farfesa, kuma wannan yana bani dariya, amman hakkan yana sa ni jin dadi a zuciyata. Duk da ina gaya ma masu gaskiyan cewan, sekandare ne kawai nayi. Na samu awards uku akan rubutu, kuma ina cikin iyayen kungiyoyi biyu manya. Kungiyar Gizago da Alkalam, Marubuta. Na zama mai ba da shawara a kafa da yawa, akan zamantakewa da aurataiya.

SHAWARAN MAHAIFA

Mahaifiyata ta rasu tun ina sakandare school kuma daya ke yar fari ce ni, ba ta cika dogon magana da ni ba, amma mahaifina baya wasa da bani shawarwari akai akai. Daya daga cikin shawaran da ya faye bani shine, cewan duk abin da kayi, ko sharri ko hairi zai dawo maka. Wannan abu yana bani tsoro a rayuwa. Kuma ya ce mani aure a kullu yaumin yafi rashin auren.

TARBIYYAN WANNAN ZAMANIN

Gaskiya kam wannan zamani yana da ban tsoro. Dalilin wannan tsoro da na kan ji na zamani shine, RASHIN KUNYA da ya zama ruwan dare. Wannan abu yana ba sa’oinmu alajabi ainun, domin mukan tattauna kan hakkan. Kuma abin da na lura shi ne, iyayen yaran basu damu da koya wa yaran su muhimmancin KUNYA a aikace, ko a tunani ba. Kunya yana kawo ragowa, da cigaba domin ko don kunyar a so mutun.

Amma ina?

HANYOYIN DA IYAYE YA KAMATA SU BI WAJEN TARBIYYA

Na farko dai iyaye su rinka kusantar yayan su mussaman mata, suna jin damuwar su. Iyaye su rinka musayan ra’ayi, su rinka yarda da su fadi yaro ya fadi. A ba yara dama su fadi damuwar zuciyar su, ba wai dole ne ace wai baza suyi magana ba, don kada ace sun yi raini ba. A nemi yaro, ya fada abin da zai fadi, saboda a san abin da ke damun sa a ko da yaushe.

Na biyu a basu Yancin su tare da yi masu kashedi akan yadda gaskiya da tsoron Allah Kawai, zai fidda su a ko ina kuma ko wane lokaci. A cigaba da gaya masu Allah. Idan anyi haka yaro ba zai bijire ba, kuma ko ya fara zai tausaya wa iyayen shi. Idan sun zama abokan shi.

KAFOFIN SADA ZUMUNTA

Ai wadannan kafafe, sune duniyar ta mu ta BIYU!Watau su facebook, twitter, instagram da sauran su. Ta irin wannan duniyar ba abin da baza iya yi ba. Za’a iya yin neman kudi, za’a iya neman ilimi za’a iya yi mu’amula na arziki kala-kala. A ganina, kafa ce da za’a iya haduwa ayi aure da mu‘amula masu kyau. Yanayin mu’amular ka, yanayin HALIN ka. Har da na rashin arzikin Allah Sawake.

Idan dai ana tsoron Allah, kuma an kiyaye dokokin Shi babu komai na illa duniyar gizo, kuma akwai amfani matuka.

KALUBALEN DA NA FUSKANTA A KAFAR SADARWA

Da farko dai kafin a kai ga sani na, shekaru takwas da na fara mu‘amula da jama’a, naga abu! Wani lokaci idan nayi magana sai wani ya shirga mani rashin kunya yace karya ne ko ba haka bane, karya nake yi. Ina da masu gyara mani magana, ko suce ban iya hausa ba, kuma su tambaya cikin rashin da’a ni wace yare ce? Na sha rashin kunya matuka wajen yaran da na haifa mussaman. A lokacin, mutane da yawa suna fita daga facebook, inda na fi zama, ko da yaushe saboda rashin da’an mutane. Amma ni dai na jure. Akwai lokacin da zan ga a shafina in ga an rubuta, ‘ke kina da aure’ amma kina facebook don neman maza.’ An sha yi mani haka. To da juriya da addua,na kai kamar yanzu da Alhamdulillah tafiya tana kyau.

MU’AMALATA DA MUTANE

Mu’amula ta da mutane ya danganta da halin da na samu kaina a ciki, watau yanayin mu’amulan nake nufi. Yawancin mu’amular da nake da mutane, na nuna kauna ne,da tausayawa tare da tattauna wa akan matsalolin rayuwa. Muna zumunci kwarai da gaske da yawancin su, kamar kashi tara cikin goma. Kuma yawancin abokan mu’amula na kashi takwas cikin goma matasa ne, saboda suna koyon darrusa akan soyayya da aure. Matsalan wadannan matasa, kusan mastalata ne, haka nake gani. Muna muamula na uwa da ya’yan ta,a wannan kafa na facebook kuma Alhamdulillah na samu karbuwa.

MAGANAN DAIDAITO TSAKANIN MAZA DA MATA

E, to a gaskiya basu burge ni ba! Domin suna son karfafa abin da bai kamata su karfafa ba. Nasan wannan magana na daidaito yabi duniya tabbas, amma barnar da maganan ke yi a al’ummah yafi gyaran da yake yi. A kullum ina lura cikin labarai, ko tattaunawa da ake yi a kan wannan lamari na daidaito. A gaskiya ina murna da tallafin da ke ba matan mu a matsayin taimako, amma bana jin dadin yadda suke bijire wa zama da ladabin aure, a sakamakon hakkan ba. Mata da yawa a wannan lokaci suna neman su fi karfin mazajen su, saboda wannan maganan daidaito. Ni a ra’ayina, har yanzu ban yarda da cewan za’a samu daidaito ba, kuma ko an samu kuwa abubuwa baza su tafi dai dai ba kuwa. Turawa ne kawai suke son su bata mana alada,kuma su kashe mana addini.

Meyasa nace hakkan? Saboda ai addini yakamata ya zama yafi karfin komai rayuwa. Shi ne gaba. Addinin mu kuwa bai yadda da cewan maza suna cutar mata ne ba, don ba daya suke ba. Addini ya ba kowa hakkin shi. Mace, mace ce kuma namiji namiji ne.

Zaman mace a matsayin maikaciya ko mai neman nata ba laifi bane…amma mace ta zama komai nata kamar na namiji laifi ne domin aure zai daina tasiri. Wannan kuwa ba zai yi mana kyau ba nan gaba.

SHAWARA AKAN NEMAN NA KAI

Tabbas lokaci ya riga ya zo, inda mata yakamata su ma su tashi tsaye akan neman na kan su. Ya Allah Dinki, koyarwa, likita da saura ayyuka na neman na kai. A wannan zamanin da wayewa ya hasko, kuma yawancin mata sun yi nisan makaranta, dole ne su ma su bada irin nasu gudunmuwar a alummah saboda a samu saukin rayuwa. A wannan zamanin bukatun mata ya kara yawa, saboda haka zai taimaka , mace ta samu na kan ta ko ba komai. Balle ma idan tana taimakawa zaman aure zai dadi. Kuma idan aka rasa auren ana iya kula da kai, ba tare da wahalar da kai, ko iyaye ba.

A kuma hankali da cewan kada nema ya hana mu aure.

ILIMIN MACE

Tabbas idan aka ilmantar da mace an ilmantar da alummah gaba daya, tunda mace uwa ce. Ina goyon bayan ilimin mace, tare da fatar ba zata raina mijin ta ko sauran jama’a a dalilin haka ba. Mace mai ilimi kuma tare da aiki da ilimin tafi kowa tsada a duniya.

LALACEWAR MA TA A MAKARANTAR GABA

Da yake duk wani wayewa da koyi, akan fara shi ne daga sakandare, idan kuma an samu zuwa gaba, to zai cigaba! Saboda haka, dole ne ince tarbiyan da aka samu a gaba da sakandare, yakan bi mutun har zuwa ga tsawon rayuwan shi, amma idan aka samu daman kai wa jami’a gaba da sakandare, to ko menene mace ta iya da sakandare, zata cika shi a gaba idan ta kai da. Anan ne dalibi yakan fara saitin shin wani irin mutun ne zai zama. Yawanci anan ne ake fara koyon yawace yawacen banza da ke da wuyan bari.

Saboda haka akwai maganan koyi da wasu dabiu marassa kyau, daga kawaye da abokan muamula… kamar shaye shaye, karya, bin maza, da uwa uba madigo. Wannan madigo yana da lahani sosai a rayuwan ya mace. A kan haka ne takan kasa ganin tasirin da namiji, a sha’anin aurataiya. Daga haka ne ake lalacewa har mace ta saba da daukar mace yaruwar ta abokiya muamular da za’a yi da miji, wannan yana hana aure, ko ya bata shi, a yadda ‘yancin na na mata yayi yawa.

Kuma abin bakin ciki na wasu yana dorewa, ya bisu har tsawon rayuwar su. Zai yi kyau a daina makarantar kwana a rinka barin kowa yayi tarbiyan diyar shi a gida.

Amma ra’ayina ne.

SHAWARA GA MATAN AURE DA YAN MATA

Shawarata ga mata gaba daya shi ne aji tsoron Allah! Akwai wasu dabi’un da yake zama mu kadai muka iya su, kuma muyi mursisi kamar ba mu ba. Yaudara da rashin hankuri! Duk inda namiji ya kai ga yaudarar shi, bai kai mace ba. Saboda ita ce tafi namiji iya chanja yanayi, ko kala tamkar hawainiya ba tare da an gane ta ba. Amma namiji ana gane shi da wuri. Don Allah Mata mu sani cewan Allah yayi mana baiwa ne, ba don mu cutas da wasu ba. A ganina, idan mace ta koyi yin hankuri da irin halin da tasamu kan ta a ciki, to zata girbi alheri, amma idan tace kyashi zata sa a gaba, to tana da aiki. Yan uwana mata, wannan hali da ake jinjina mana na rashin godiya, mu bar shi. Shi yake kashe mana aure. Kuma shi yake hana wasun mu auruwa…don ana gudun a aure mara godiya, tayi ta tara wa miji gajiya.

Mata mu rage son abin duniya mu koyi hankurin jiran lokaci, kada mu je mu hallaka kan mu garin kwadayi da cewan sai munyi kitson wance ba, bayan bamu da gashin wance ba. Daga karshe zan yi wa mata huduba a kan kishi. Yakamata mu san kishi ba hauka bane.

Kuma duk kishin ki bazaki hana namiji neman wata ba, ko da aure ko ba auren ba, amma abin da yakamata kiyi shine, ki zama mashi tauraruwa a idanuwar shi, kafin ki shige zuciyar shi gaba daya… da sai dai ya kalli mace a ido, amma ba wai ya tahalike mata ba. Amma idan neman aure ne ki daure, mai hali shi zai karbe miji, kuma kullum ki zauna danshirin cewar zai iya aure saboda haka ki yarda da kanki ta gyara hali da tsabta tare da addua a ko da yaushe na kawar da sharrin dayake tsakanin ki da mijin ki. Don Allah matan aure a daina wulkanta yannuwan miji tun ba idan yana da kudi ba.

Ita kuma mace mara aure, ba ki matsa da neman namiji na kirki ba, ke ma ki zama na kirki. Ki rage fadin rai don kina da kyau domin duk da maza suna da shaawa, msuna kuma da hankalin neman mai kyaun hali. Mace kina so a so ki na ainihi?

To ki rage girman kai,ki iya bada hankurimidan kinyi laifi, ki rage son kai, ki rage bincike da zargi,ki rage karya da korafi. Idan kin gyara halin ki zai so ki, idan bai so ki ba to shiyake da matsala ba keba, sai ki gaya wa Allah.

ABINCI

Abincin da nafi so shine tuwon alkama miyan kuka.

TUFAFI

Tufafin da nafi so shine shadda tun ba idan anyi mashi barnina ba!

TAURARUWA TA?

Tauraruwata ita ce Aisha Buhari.

KOYIN DA NAKE YI DA ITA.

Ina koyi da fadiwa mijinta gaskiya komin dacin shi, tare da yunkurin fin karfin halin zama da jamaa kala kala, tare da juriyan gwagwarmaya da mutane.

GUDUNMUWATA GA AL’UMMA

E to, bana son yabon kai na amma ina iya kokarina tun ba a kafan yada zumunta da rubuta littafai zuwa hiran talabijin ba.

Littafin da na taba karantawa a rayuwa da naji dadi, kuma nayi koyi da shi;

shine RUWAN RAINA na Amina Abdulmalik.

Wannan littafi ya taba motsin zuciyata kwarai akan yadda ake rayuwa na yarda da lumana, kuma na cikin haka Allah Yayi Na shi ikon. A wannan littafin ne na ga yadda ake nuna wa juna kauna na zahiri ba na karya ba, kuma da yadda alummah yawanci basu gane irin wannan kaunan. Sai ayi tsammanin shiririta ne saboda yayi kama da karya. Na koyi darussa da yawa a cikin wannan littafin. Darussan harda da sanin cewan komai yayi farko zaiyi karshe, kuma soyayya gaskiya ce.

2 comments

Leave a comment